Mutane 26 a Berlin sun jikata bayan wani saurayi ya kai musu hari da wuka | Labarai | DW | 27.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 26 a Berlin sun jikata bayan wani saurayi ya kai musu hari da wuka

Wani matashi a birnin Berlin ya dabawa akalla mutane 26 wuka inda yayi wa wasu daga cikin munanan raunuka. Hakan ya faru lokacin da mutanen ke barin wurin bukin bude sabuwar babbar tashar jirgin kasa ta farko a birnin na Berlin. Saurayin dan shekaru 17 da haihuwa ya fara wannan ta´asa ne da misalin karfe 12 dare. ´Yan sanda sun ce mutum 6 daga cikin wadanda ya dabawa wukar na cikin wani mummunan hali bisa raunin da suka samu. ´Yan sandan sun kara da cewa saurayin na da tarihin tashe tashen hankula kuma yanzu haka yana tsare. Tashar jirgin kasar dai ita ce mafi girma a Turai, wadda zata iya daukar jiragen kasa sama da dubu daya da kuma fasinjoji kimanin dubu 300 a kowace rana.