Mutane 19 ne suka mutu a harin Nyanya | Labarai | DW | 02.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 19 ne suka mutu a harin Nyanya

Kwana daya bayan tashin bam a tashar mota ta Abuja, an tabbatar da cewa mutane 80 ne suka samu raunuka, yayin da kusan 20 suka bakwanci lahira.

Hukumomin tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 19 a harin bam da aka kai a tashar mota ta Nyanya da ke birnin Abuja. Kakakin rundunar 'yan sanda Frank Mba ne ya bayar da wadannan alkaluma lokacin da ya yi bayani a inda bam din ya tashi. Da ma dai tun da farko hukumar kai agajin gaggawa ta NEMA ta nunar da cewa mutane 80 ne suka samu raunuka sakamakon tashin bam din na ranar Alhamis. Sai dai kuma rundunar 'yan sanda ta ce an gano wasu bama-bamai uku da ba su tashi ba a tashar motar a wannan rana ta jumma'a.

Babu dai wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin. Sai dai kuma Kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ta ce ita ce da kai makamancin wannan hari a watan da ya gabata a tashar mota ta Nyanya. Wadannan hare-hare dai na afkuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan kafin birnin Abuja ya dauki bakwancin taron tattalin arziki na kasa da kasa, wanda ake sa ran shugabannin duniya da dama za su halarta.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu