Mutane 17 sun rasu a tashin hankali a arewacin Najeriya | Labarai | DW | 29.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 17 sun rasu a tashin hankali a arewacin Najeriya

Rahotanni daga garin Bama dake jihar Borno sun ce wata musayar wuta da aka yi tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Wani jami'in soji a tarayyar Najeriya ya ce an halaka akalla mutane 17 a wani fada da aka gwabza tsakanin 'yan bindiga da dakarun tsaro a yankin arewa maso gabacin tarayyar ta Najeriya. An gwabza fadan ne a garin Bama dake a jihar Borno, inda tun a shekarar 2010 'yan bindiga ke fafatawa da dakarun gwamnati. Laftanan Kanal A.G. Laka ya fada a wannan Litinin cewa fadan yayi sanadiyar mutuwar jami'an 'yan sanda bakwai da kuma 'yan bindiga 10. 'Yan jarida da ke wa wata tawagar gwamnati rakiya a yankin sun ce ba su ga gawa ko guda daya ba, sai dai sau da yawa sojoji a Najeriya na rage yawan wadanda irin wannan tashin hankali kan rutsa da su. Wani dan jarida ya ce an kona gidaje da kuma shaguna da kuma wuraren kasuwanci.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar