1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 15 za su yi takara a Nijar

Usman Shehu UsmanJanuary 9, 2016

Kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar ta yanke hukuncin amincewa da takaran muta ne 15 ciki harda Hama Amadou wanda ke tsare a halin yanzu

https://p.dw.com/p/1HanS
Niger Mahamadou Issoufou und Hama Amadou
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Kotun kundin tsarin mulki a jamuhuriyar Nijar, ya yasanar da cewa fitaccen dan adawan kasar Malam Hama Amadou na da cikin jerin wandanda za su yi takaran shugaban kasa a zaben kasar da ke tafe. Kotun a hukuncin da ta yanke yau Asabar 10.01.2015, ta amince da takaran shugaban kasa ga mutane 15, a ciki harda Hama Amadou wanda ya kwashe lokaci yana hijira wejen kasar. A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, amincewar da kotu ta yi ga takaran Hama Amadou zai zama kalubale da mastin lamba kan gwamnatin Nijar, ta sako Hama wanda hukumomi suka daure shi tun bayan komar warsa gida. Yanzu dai bisa hukucin da kotun ta yi, mutane 15 kenan za su yi takaran shugabancin jamhuriyar Nijar a zaben ranar 21 gawatan gobe.