Mutane 1200 sun ƙaurace wa matsuguninsu bayan tashin hankali a Bama | Labarai | DW | 03.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 1200 sun ƙaurace wa matsuguninsu bayan tashin hankali a Bama

Tun bayan tashe tashen hankullan da suka biyo bayan rikicin addini a kasar Bama ko kuma Miyanmar,kungiyoyin kare hakin bil Adama na nuna damuwarsu a kan lamarin.

Kungiyar 'yan gudun hijira ta duniya ta bayyana matuƙar damuwarta bisa ga yadda hukumomin ƙasar Bama ko kuma Miyanmar suka fuskanci matsalar 'yan gudun hijiran yankin Rahkine a yammacin ƙasar bayan rikicin addinin da ya ɓarke mako ɗaya da ya shuɗe.
Rahotanni dai sun bayyana cewar sama da mutane 140 ne suka rasa rayukansu sakamakon tashe tashen hankulan da suka biyo bayan rikicin addini tsakanin mabiya addinin Budah da kuma musulmai a kasar inda hasali ma aka goge wani garin musulmin kwata kwata daga doron ƙasa. Dama dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana musulman Bama a matsayin jama'an da ta fi fuskantar tsangqwama a duniya. An nunar cewa mutane kimanin 1200 suka ƙaura wa matsugunansu bayan tashin hankalin na addini.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita : Mohammad Nasiru Awal