Mutane 120 ne suka rasa rayukan su a iraqi | Labarai | DW | 05.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 120 ne suka rasa rayukan su a iraqi

Mutane a kalla 120 ne suka rasa rayukan su a Iraqi a sakamakon hare haren bama bamai a kasar a yau Alhamis.

Daga cikin wannan jumla ta sama, an shaidar da cewa mutane biyasr ne yan kasar Amurka suka rasa rayukan su.

Rahotanni sun kuma shaidar da cewa wasu mutanen sama da dari biyu ne suka jikkata a sakamakon faruwar wannan abu a ranar ta yau alhamis.

An dai fuskanci tashe tashen bama baman ne na yau a garuruwan Kerbala da kuma Ramadi, guraren dake da magoya yan shi´a da yawa a cikin sa.