Mutane 12 sun tsira daga hadarin jirgin sama a Indonesia | Labarai | DW | 02.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 12 sun tsira daga hadarin jirgin sama a Indonesia

A kasar Indonesia mutane 12 sun tsira da ransu cikin hadarin jirgin saman fasinja daya abku jiya litinin a tsibirin Sulawesi.

Fasinjoji 90 sun rasa rayukansu bayanda jirgin na kanfanin Adam air yayi hadari sakamakon rashin kyan yanayi.

Matukin jirgin dai ya aike signa na neman agaji kafin jirgin ya bace daga kann naurar hangen jirage na filin jirgi daya tashi.

A halinda ake ciki kuma,a birnin Java ya zuwa yanzu an samo mutane 191 da ransu bayan hadarin jirgin ruwa a kasar ta Indonesia,wasu kuma 400 har yanzu baa gano suba.