Mutane 102 ne suka mutu a harin Nijar | Labarai | DW | 04.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 102 ne suka mutu a harin Nijar

An kara samun gawawwaki a wuraren da aka kai harin karshen mako a Jamhoriyar Nijar.

Hukumomi a Jamhoriyar Nijar sun sha alwashin kara yawan dakarun sojin kasar a yankin da aka hallaka fararen hula a karshen mako, bayan da aka kara samun gawawwaki biyu a wurin da abin ya faru.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ce ta tabbatar da samun karin wadanda harin ya rutsa dasu, wanda kuma ya daga alkalumman mamatan ya zuwa dari da biyu kawo yanzu.

Nijar din za ta kafa wani sansanin soji na dindindin a yankin, in ji Mammane Sani kwamandan rundunar sojin da ke yaki da 'yan bindiga a yankin.

Tuni dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin kuma ya bukaci daukar kwakwkwaran mataki kan wadanda aka samu da hannu cikin wannan aika-aikar.