Musulmi na taya Kiristoci murnar Kirsimeti | Siyasa | DW | 24.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Musulmi na taya Kiristoci murnar Kirsimeti

A wani mataki na karfafa kyakkyawar dangantaka da zumunci tsakanin Kiristoci da Musulmi a Tarayyar Najeriya, al'ummar Musulmi da malamansu na ta ya kiristoci murnar bukukuwan Kirsimeti.

Al'ummar Musulmin dai na amfani da kafafen sadarwa na zamani irinsu sakonnin SMS a wayar Salula da Facebook da Twitter domin aikawa Kiristoci sakwanni na gaishe-gaishen bikin zagayowar ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S). Alaramma Abdul-Rahman Mohammad Bichi na daya daga cikin malaman makarantun Allo a yankin Barnawa da ke kudacin jihar Kaduna, yace sun ma kaiwa malaman Kiristocin kyaututtuka na Kirsimeti Irin su Abinci da tufafi dama dabbobin da za su yanka domin kara kulla dankon zumunci tsakanin Musulmi da Kiristocin da ke fadin wannan kasar da kuma kawo karshen rashin fahimtar koyarwar addinan guda biyu.


Rera wakokin Kirsimeti tare da Musulmi

Wakokin bikin Kirsimeti daban-daban ne matan Kiristoci tare da na Musulmi suka raira a gidan wani babban Limamin Coci da ke zaune a yankin kudancin Kaduna, domin kara tabbatar da dorewar zaman lafiya tsakanin addinan biyu. Yayin da a wani bangaren kuwa wasu Kungiyoyin Musulmi suka fara kaiwa Kiristoci ziyara da kuma rarraba musu kyaututtuka iri-iri don karfafa kyakkyawar dangantaka tare da kawar da kyamar juna domin magance rigingimun da ke da nasaba da addini da suke janyo koma baya a cikin kasar saboda gurguwar fahimtar koyarwar addinan. Wannan dai shine karo na farko da bangarorin biyu ke kaiwa juna ziyara, tun bayan rikicin addini da ya rarraba kawunan Musulmi da Kiristocin jihar Kadunan. Hajiya Maryam Abubakar ita ce shugabar kungiyar mata Musulmi daga jihohin arewa, kana ita ce ta jagoranci kai ziyara ga gidajen Limaman coci-coci domin rarraba masu kayayyakin abinci a Majami'un tare kuma da shiga unguwannin Kiristoci domin kara kulla dankon zumunci, ta kuma ce.

Muslmi sun ziyarci Kiristoci

"Daga wurare masu nisa muka fito domin zuwa kulla zumunci da Kiristoci a wannan lokaci, ya zamo wajibi mu kawar da ban-bance-ban-bancen da ke tsakaninmu domin taimakawa hukumomi da kungiyoyi a fafatukar da suke yi na bunkasa tattalin arzikin kasa da dorewar zaman lafiya tsakanin mabanbanta addinai da kabilu."

Shi kowa Malam Lawal Muduru wani babban malamin addinin Musulunci a Najeriya ya je gidan Kaso ne inda ya 'yantar da Kiristoci masu yawa domin su yi bikin Kirsimetin a cikin iyayelensu. A nasa bangaren daya daga cikin manyan malaman addinin Kiristan a Najeriya Pastor Yohanna Buru cewa ya yi......

"A rayuwata ban taba ganin irin wannan abu ba irin mutuncin da Musulmai suka yi mana mazansu da matansu sun zo gidana da Coci na domin ta ya Kirista gyara itacen Kirsimeti da kuma kwaskwarimar da ake yi wa Coci-coci."

Ya zuwa wannan lokaci dai, matasa Musulmai sun sha alwashin kare Majami'u daga farmaki da kuma taimakawa Kiristoci da tsaro yayin bukukuwan na Kirsimeti

Sauti da bidiyo akan labarin