Musulman duniya na shagulgulan Sallah | Labarai | DW | 08.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musulman duniya na shagulgulan Sallah

A faɗin duniya an gudanar da bikin ƙaramar Sallah, bayan kammala azumin wata Ramadan

Das Ramadanfest ist ein islamisches Fest zum Abschluss des Fastenmonats Ramadan. Foto: Aminu Abubakar Abdullahi, Nigeria, 08.08.2013

Hawan Idi aSokoto

Ayayin da ake ci gaba da shagulgulan Sallah cikin ƙasashen duniya, a jihar Kano dake arewacin Nigeria, a bana ma dai al'ummar jihar na cewar sallar ta bana babu armashi, duba da zaman fargaba da ake ciki, kana kuma da rashin gabatar da hawan Sallah da sauran shagulgulan sallah da a duk shekara suke kawata bikin. Rashin hawan sallar dai baya rasa nasaba da kasancewar sarkin Kano yana fama da rashin lafiya, wacce ta tilasta masa fita kasashen waje domin yin jinya, lamarin da ake ganin ya taimaka wajen dakushe armashin sallar ta bana.

Titel: Ado Bayero, Emir von Kano/Nigeria Schlagworte: Kano, Nigeria, Emir, Bayero Wer hat das Bild gemacht?: Thomas Mösch Wann wurde das Bild gemacht?: 27.5.2008 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Kano / Nigeria Bildbeschreibung: Bei welcher Gelegenheit / in welcher Situation wurde das Bild aufgenommen? Wer oder was ist auf dem Bild zu sehen? Ado Bayero ist seit 1963 Emir von Kano. Er wurde am 15. Juni 1930 geboren und ist einer der wichtigsten traditionellen Führer Nigerias. Bildrechte: (Grundsätzlich nur eine Variante möglich, Nichtzutreffendes bitte löschen.) Der Fotograf ist (freier) Mitarbeiter der Deutschen Welle.

Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero

Sallar Kanawar ba hawan taushe

Bikin salla a jihar Kano dai a iya cewa babu yabo kuma babu fallasa, idan aka yi la'akari da yadda aka gabatar da shi a yau Alhamis, duk da cewar an sami fitowar dubun-dubatar mutane domin halartar sallar Idi, amma galibi mutanen na cikin fargaba, musamman ganin jamian tsaro dake jibge a masallatan. Wani abu da shi ma ya kara ruruta fargabar shine sanarwar da rundunar tsaro ta farin kaya wato SSS ta bayar, na cewar mutane su yi hattara wajen kula da masu shiga da fita a wuraren ibadun. Darektan hukumar a jihar Kano Etang Bassey ya yi nuni da cewar akwai yiwuwar hare-hare a wuraren ibadu.

Das Ramadanfest ist ein islamisches Fest zum Abschluss des Fastenmonats Ramadan. Foto: Aminu Abubakar Abdullahi, Nigeria, 08.08.2013

Mahaya Rakuma a Sallah idin Sokoto

"Kada abar mutane su ringa shiga da wasu abubuwa da ba a amince da su ba zuwa wuraren ibadu, wanda za su iya kasancewa abubuwan da za su iya haddasa asarar rayuka. La'akari da abubuwa da suke faruwa akwai bukatar hadin kai da limamai, domin sanya idanu dan ganin an killace duk wani abu da ba a amince da shi ba daga cikin masallaci, kafin ya kai ga yin barna.

Matakan tsaro yayin shagulgulan Sallah

Wani abu da shi ma ya kara dakushe armashin sallar bana a Kano, shine rashin hawan salla, kasancewar a bana sarkinn Kano ya fita kasar waje domin jinya, hakan yas a masauratar jihar ta bada shelar dakatar da yin hawan salla, dama duk wani shagali da aka saba gabatarwa, lamarin da wani mahayin doki maisuna Jazuli Ibrahim yace garesu sallar ta bana bata wuce lami ba.

Das Ramadanfest ist ein islamisches Fest zum Abschluss des Fastenmonats Ramadan. Foto: Aminu Abubakar Abdullahi, Nigeria, 08.08.2013

Hawan Sallar Idi a Sakoto

Ibrahim Abubakar magidanci ne a birnin Kano, wanda shi ma ke ganin Sallar bana ta zo musu a hagunce, dan haka babu wani armashi.

Itama dai anata bangaren rundunar 'yan sandan jihar ta Kano, ta bayar da shelar haramta duk wani ciniki a cikin masallatan Idi, bisa zargin cewar harin baya da aka kai cikin yankin Sabon Gari, an fake ne da yin tallan Kankana da Dabino a cewar rundunar, lamarin da shi ma ya kara jefa fargaba a zukatan alumma. Sai dai duk da rashin armashi da bukukuwa a yayin sallar, wasu 'yan tauri ba su fasa gabatar da kade-kadensu na al'ada ba .

Mawallafi: Nasiru Salisu Zango

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin