Musulmai sun fara azumin watan Ramadan na bana | Labarai | DW | 06.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musulmai sun fara azumin watan Ramadan na bana

Musulmai a galibin kasashen duniya sun tashi da azumi a wannan Litinin sakamakon ganin jaririn watan Ramadan.

Galibin Musulmai a kasashen duniya sun fara azumin watan Ramadan da ya daga cikin muhimman rukunan addinin. A ranar Lahadi mahukunta a Saudiyya sun bayyana cewa sakamakon ganin jaririn watan Musulmai a kasar sun tashi da azumin a wannan Litinin.

Kuma akwai kasashe da dama na Musulmai da suka bayyana haka, ciki har da Najeriya. A karshen watan za a yi bukukuwa na Sallah.