1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar musulmai a sansanin Auschwitz

Suleiman Babayo AAI
January 23, 2020

Kawo yanzu musulmai kalilan suka taba ziyarar sansanin gwale-gwale na Auschwitz-Birkenau da ke kasar Poland na 'yan Nazi na Jamus lokacin yakin duniya na biyu inda Yahudawa masu yawa suka dandana kudarsu.

https://p.dw.com/p/3Wivh
Angela Merkel da tawagarta a sansanin gwale-gwale na Auschwitz
Angela Merkel da tawagarta a sansanin gwale-gwale na AuschwitzHoto: Reuters/K. Pempel

A wajen da yanzu haka ke kasar Poland masu mulkin Jamus karkashin jagorancin 'yan Nazi sun kashe kimanin Yahudawa miliyan 1.1 lokacin yakin duniya na biyu har zuwa shekarar 1945. Raed Saleh wanda yake cikin 'yan siyasa na Jamus karkashin jam'iyyar SDP a matsayin dan majalisa a shekara ta 2013 tare da matasa, sun ziyarci wannan sansanin gwale-gwalen. Duk da haka akwai karancin Larabawa daga cikin adadin maziyarta kimanin 3,200 kacal a cikin alkaluman a hukumance. Sai dai shugaban kungiyar kasashen Musulmai ta duniya Mohammed Al-Issa kana tsohon minista a gwamnatin Saudiyya ya kai ziyara sansanin tare da David Harris shugaban Yahudawa na Amirka wanda iyayensa suka tsira daga wannan azaba. Sannan shugaban kungiyar kasashen Musulmai ta duniya Mohammed Al-Issa ya bukaci daukacin Musulmai su goya daga abin da ya faru a tarihi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Rahotanni da Sharhuna

Rahotanni da Sharhuna