Musulmai a kasashen Najeriya da Nijar sun kawo karshen Azumi | BATUTUWA | DW | 04.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Musulmai a kasashen Najeriya da Nijar sun kawo karshen Azumi

Musulman da ke kasashen Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun kawo karshen Azumin bana tare da gudanar da bukukuwan Sallah cikin kwanciyar hankali.

Jama'a a yankunan da ke fama da hare-haren 'yan bindiga a jahohin Katsina da Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun gudanar da Sallar Idi sai dai sun gudanar cikin dar-dar dan gudun abin da ka iya faruwa.

Yankuna da dama sun gudanar da Sallar Idin sai dai babu walwala musamman yadda jama'a ke cikin talauci saboda irin yadda 'yan bindiga suka lalatawa.

Sakamakon yawaitar kashe-kashen al'umma a jihar Katsina masarautun Katsina da Daura sun soke gudanar da shagulgulan da suka sabayi duk shekara da nufin nuna alhini ga wadanda suka rasa rayukansu. A bangaren jami'an tsaro a jahohin Katsina da Zamfara tun kafin sallar sun fitar da sanawar ba da tsaro ga jama'a dan ganin kowa ya samu damar yin sallar.

Haka a Jamhuriyar Nijar duk da barazana na tsaro da hukumomi suka yi gargadi an gudanar da bikin cikin tsanaki da kwanciyar hankali.

Sauti da bidiyo akan labarin