Musayar yawu a zaben Bahrain | Labarai | DW | 23.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musayar yawu a zaben Bahrain

Abinda aka fi maida hankali a kansa na zama rashin fitowar masu kada kuri'a, lamarin da ake dangantawa da cewa zai shafi sahihancin sakamakon zaben 'yan majalisar.

Musayar yawun dai na ci gaba da tsamari a dangane da zaben kasar Bahrain a ranar Lahadin nan tsakanin 'yan sunni da ke jan ragamar kasar da 'yan Shia wadanda suka kauracewa zaben, inda aka samu karancin wadanda suka fito dan kada kuri'a da ma danganta zaben da tafka kura-kurai a cikin sa.

Duk da cewa ana ci gaba da kidaya kuri'un zaben majalisar mai wakilai 40 har yanzu abinda aka fi maida hankali a kansa na zama rashin fitowar masu kada kuria lamarin da ake dangantawa da cewa zai shafi sahihancin sakamakon zaben.

Hukumar zaben kasar dai ta bayyana cewa an sami sama da kashi 51 daga cikin dari na wadanda suka fita kada kuri'a, amma acewar bangaren 'yan shia kashi talatinne cikin dari suka fita dan kada kuri'arsu.

A yayin da bangaren 'yan sunni ke zargin 'yan shia da hana mutane karasawa zuwa tashoshin kada kuri'a, su kuwa 'yan shiar na cewa dubban mutane ne ake tilasta musu su kada kuri'a ba dan suna da muradi ba.

Wannan zaben 'yan majalisar na zama karon farko tun bayan da jami'an tsaro suka murkushe wata zanga-zanga a shekarar 2011 ta neman sauyi a wannan daula da 'yan sunni ke wa jagoranci, zanga zangar da 'yan shia suka jagoranta.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu