Musayar kudade ta hanyar wayar salula a kasar Ghana | Zamantakewa | DW | 26.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Musayar kudade ta hanyar wayar salula a kasar Ghana

Tura kudi ta wayar salula na tafi da gidanka ya saukaka harkokin kasuwanci ga kananan yan kasuwa, sai dai kuma yan kasuwar na korafi kan yawan kudin da kamfanonin sadarwar ke caza.

Kamfanonin sadarwa na wayar salula sun bullo da hanyoyin musayar kudade irn na tafi-da-gidanka ta wayar salula da zummar rage wahalhalu da ake fuskanta a  fannoni kananan kasuwanci, kana mutane suma kan tura kudi ga 'yan uwa da abokan arziki lokacin bukukuwa kamar na kirsimiti, to sai dai wasu na ganin kamfanoni da ke lura da tsarin na ci da gumin masu amfani da wannan hanya ta tura kudaden saboda cire kashi daya cikin dari na yawan kudin da ake turawa ga mai karba kafin a tura masa. 

A birnin Tamle na kasar Ghana shagulgulan kirstimeti, lokaci ne na kasuwanci da mutane da dama, musamman mabiya addini kirista ke sayayyar kayayyaki da ma tura kadade ga 'yan uwa ta wayar salula.


Ghana Geldscheine Cedi (imago/Xinhua)

Tura kudi ta hanyar wayar salula a Ghana

Sai dai kuma mutane kamar Maimuna yahaya wacce ta saba tura kudi ta waya na korafi kan yawan kudin da kamfanonin sadarwar ke caza. 

''Idan ka tura kudi ko kuma aka turo maka sai ka biya, kuma idan baka da kudi a asusun ajiyar ka za su cire daga cikin kudin da za ka tura, amma idan akwai kudi a asusunka baza su cire daga cikin kudin da ka tura ba''

Tsarin tura kudin ta wayar salula dai ya samu karbuwa a kasar Ghana. kamfanin wayar salula na MTN a kasar na daya daga cikin kamfanonin da ke samar da wannan tsari na tura kudi inda yake da dillalai dubu tamanin da biyar a fadin kasar wanda ya dara yawan bankuna a cikin kasar a halin yanzu. Sai dai wasu na sukar tsarin da ci da gumin 'yan kasar inda suke cewa gwamma tsarin da aka saba da shi na bankuna. Abdul Majid Rufai shine Manajan sashen lura da bunkasa  kasuwanci ya kuma kare wannan tsari na tura kudi ta wayar salula

Ghana Accra - Markt (picture-alliance/ZB/T. Schulze)

Hada hadar kasuwanci a kasuwar birnin Accra

.

''Duk kudin da ya haura Cedi hamsin in za a tura to ana biyan kashi daya cikin dari na yawan kudin da za a tura, ga misali idan za a tura Cedi 1000 na Ghana to za a biya Cedi goma, Cedi dubu biyu zuwa dubu hudu duk Cedi goma a ke biya, babu yadda za a caje ka sama da Cedi goma a wannan tsarin''  

Yawan kudin da ake caji a wannan tsarin shine kawai matsala, a baya-bayannan bata gari na amfani da tsarin wajen damfarar 'yan kasar ta Ghana da dama, Jonathan Kojo masanin tsaro ne a fannin yanar gizo, ya bayyana cewa yin rajistar layukan salula na daga cikin hanya da za a yiwa tufkar hanci.

Duk da irin yawan kudin da ake caji wajen tura kudaden da kuma hadarin dake tattare da tsarin, tura kudi ta wayar salula na cigaba da samun karbuwa a wajen 'yan kasar.