Musayar harbe-harbe a yankin Checheniya | Labarai | DW | 04.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Musayar harbe-harbe a yankin Checheniya

Mutane tara sun muta a wani taho mu gama tsakanin 'yan sanda da 'yan awaren checheniya a gabashin kasar Rasha.

Akalla 'yan bindiga shida da kuma 'yan sandan uku sun rasa rayukansu a wata musayar wuta da ta gudana a birnin Grozny tsakanin 'yan awaren Checheniya da kuma jami'an tsaron Rasha. Wani baban jami'in wnanan yanki ya bayyana cewar 'yan bindiga ne suka fara bude wuta a kan ayarin motocin 'yan sandan Rasha da ke sintiri inda suka kashe uku daga cikinsu. Daga bisani ne jami'an tsaro na Rasha suka rama wa kura aiyarta, inda suka kashe 'yan aware shida.

Kanfanin dillancin labaran Rasha Tass ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun ja daga a wata makaranta ta birnin Grzno. sai dai ba wanda ya ke da masaniyar ko sun yin garkuwa da wasu mutane koko a'a. Sassa biyu na kallon hadarin kaji tsakaninsu tun bayan da Rasha ta yi amfani da karfin wajen karya kashin bayan ballewa na yakinChecheniya shekaru 15 ke nan da suka gabata.

Sai dai kuma daga bisani wasu masu kaifin kishin addini sun tayar da kayar baya a wannan yanki da ya kunshi dimbin musulmi. ko da a watan oktobam da ya gabata ma dai, sai da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam dake jikinsa a birninna Grozny inda ya hallaka'yan sanda biyar tare da jikata wasu karin 12.