Muryoyin shugabannin al'umma | Shekaru 50 na sashen Hausa | DW | 28.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Shekaru 50 na sashen Hausa

Muryoyin shugabannin al'umma

"DW na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dimokraɗiyya da wayar da kawunan jama'a", - Mohamed Bazoun, ministan harkokin wajen Nijar.

Namadi Sambo, mataimakin shugaban ƙasar Najeriya:

Ina yi muku murnar cika shekaru 50 kuma ina yi muku fatan Allah ya ba ku ikon cigaba da irin wannan taimako da kuke yi na wayar da kan jama'a da kuma cigaban ƙasa. Ya kuma sake nuna mana wasu shekaru 50 ɗin nan gaba.

Mahamane Ousmane, tsohon shugaban ƙasar Nijar (1993-1996):

DW na ɗaya daga cikin rediyoyin waje da nake sauraro a kowane lokaci. Saboda DW rediyo ce da ke faɗakar da marasa ilimi har ma da masu ilimin a kan abubuwa da suka shafi rayuwa. Ina jinjina wa DW musamman a kan aikin da kuke yi na bayar da tarbiyya kyakkyawa, saboda jama'a da dama ba su iya ɗaukar littafi su yi karatu ba. Amma suna iya sauraron tasharku domin samun bayanai a kan abubuwan da suka shafi ilimantarwa da kimiyya da kare dimokraɗiyya da dai sauransu.

Seini Oumarou, shugaban jam'iyyar MNSD Nassara, tsohon firam ministan Nijar:

Rawar da kafofin yaɗa labarai suke takawa a fannin dimokraɗiyya, abu ne da ke da muhimmancin gaske. Ina tabbatar muku da cewar mun gamsu da aikin DW, saboda aikin da kuke yi ya kai mizanin abin da muke jira. Muna yi muku barka da fatan alheri da bikin cika shekaru 50 da kafuwa, kuma Allah ya ja zamaninku.

Birgi Rafini, firam ministan Jamhuriyar Nijar:

A tsawon shekaru 50 DW ta yi aikin watsa labarai kyakkyawa wanda za a iya cewar yabon gwani ya zama dole. Saboda labarun da DW ke watsawa labarai ne cikakku waɗanda ba a da shakku a kan su, ko da za a bincika. Muna taya ku murna, kuma muna jinjina muku.

Mohamed Bazoum, Ministan harkokin waje na Jamhuriyar Nijar:

DW rediyo ce mai ci gaba, wadda kuma ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dimokraɗiyya, dangane da aikin da kuke yi na wayar da kawunan jama'a da faɗakarwa, wanda kuma aiki ne da ya kamata a ce mu ne muke yi, amma ku ne kuke yin sa a madadinmu. Musamman yadda kuke gudanar da aikinku ta yadda shirye-shiryenku ke daukar lokaci mai tsawo, yakan ba mu, musamman mu masu magana, da ma mu fassara abubuwa har mutane su fahimci jawabin namu. Wannan babbar karuwa ce ga jama'a ke nan, muna so ku ci gaba da haka.

Maj. Gen. Muhammadu Buhari mai ritaya, tsohon shugaban kasar Najeriya:

Ina farin ciki da yadda kuke taimaka wa masu jin Hausa, domin kuna illimantar da su a kan siyasar duniya, da sha'anin tsaro da arzikin ƙasashen duniya, da kuma abin da zamani ke kawowa. Aikin da kuke yi na da muhimmanci sosai musamman ga ƙasashen Hausa irin su Nijar da Najeriya waɗanda ba'a sami ilimi sosai ba. Mun gode wa gwamnatin Jamus da wannan aiki da take yi.

Mrs Eneh Ede, Equity Advocates (Ƙungiyar da ke kare hakkin mata):

Kuna ƙoƙari kan batutuwan da suka shafi mata don sukan neme su, su yi hira da su, su kuma sanya shi cikin shirye-shiryensu waɗanda suke watsawa a duk duniya baki ɗaya, muna farin ciki da wannan ƙwarai da gaske.

Dr. Mariama Gamatche, mai fafutukar kare haƙƙin mata da kuma shugabar jam'iyyar Racine. Niamey, Nijar:

Muna murna da bikin cikar DW shekaru 50 da kafuwa, kuma DW rediyo ce da ta yi suna saboda ingancin labarun da kuke watsawa. Yanzu haka mutane ko da sun saurari labaru daga sauran kafofi sai sun jira DW ta bayyana; a lokacin nan suke tabbatar da cewar labarin gaskiya ne. Saboda kuna gudanar da bincike kafin watsa labari shi ya sa masu sauraro suka yarda da DW.

Ignatius Kaigama, Babban Limanin ɗariƙar Katolika a Jos, Najeriya, da kuma shugaban majalisar manyan bishop-bishop na ɗariƙar Katolika a ƙasar:

Fargaba na da ma a lokacin hargitsi ne, lokacin da akwai yiwuwar yin rahotanni masu tayar da hankali. Amma na lura da cewa babu wannan a tashar DW kuma har na sa shi a rubuce, domin a kowane lokaci idan dai ba tafiya na yi ba ina sauraron kowane shiri, na Turanci da na Hausa. Kuma ina mutunta irin dangantakar da nake da ita da tashar.

Moussa Tchangari, ƙungiyar kare haƙƙokin jama'a „Alternative Espaces Citoyens“, Niamey, Nijar:

Mun gamsu matuƙa da aikin da DW take yi na wayar da kawunan jama' a cikin yankunan karkara da birane, dangane da sanar da duniya halin da ake ciki. Sannan kuma tana ba da gudunmawarta ga ƙara ci-gaban dimokraɗiyya a cikin ƙasashensu. Mu kanmu wakilan ƙungiyoyi masu fafutuka tana taimaka mana ta hanyar ba mu damar mu bayyana abin da ake yi a cikin ƙasa na take haƙƙokin jama'a. Muna yi muku barka da cika shekaru 50.