1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mursi ya karya doka?

Halimatu AbbasNovember 23, 2012

Shugabannin adawa a kasar Masar sun yi kira da a shiga zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da matakin shugaba Mohammed Mursi na ayyanar da dokar bai wa kansa ikon yin yadda ya so.

https://p.dw.com/p/16olY
Hoto: picture-alliance/dpa

Matakin da shugaban masar Mohammad Mursi ya dauka na bai wa kansa karin iko ya haddasa shiga zanga zanga a fadin kasar har sai da masu zanga zangar suka cunna wuta ga ofisoshin jam'iyyarsa ta 'yan uwa musulmi. Kafafen yada labaru na kasashen Larabawa sun ba da rahotannin da ke nuni da cewa an cunna wuta ga ofisoshin jam'iyyar da ke a biranen Askandariya da Port Said da Suez. Sai da kuma aka murkushe wani yunkuri da aka yi domin cunna wuta ga ofishin jam'iyyar da ke birnin Alkahira. Daruruwan mutane ne dai suka yi turuwa a dandalin Tahrir suna masu zargin Mursi. To amma an kuma gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaba Mursi a gaban ginin fadarsa da ke a birnin Luxor.

Shugaban kungiyar lauyoyin kasar Masar, Sameh Ashur ya soki Mursi da take doka. Mohammed al-Baradai wanda ya taba samun kyautar zama lafiya ta Nobel shi kuma cewa ya yi Mursi ya mai da kansa tamkar sabon Fir'auna. Shi dai shugaban mai kaifin kishin Islama ya ayyanar da wannan dokar ne domin kauce wa duk wani bincike na aikin sharia akansa. Mursi ya ce babu wata kotu da za ta iya kalubalantar wannan matsayi nasa. Dadin dadawa Mursi ya kuma ba da kariya ta shari'a ga majalisar dokokin kasar da masu kaifin kishin Islama ke da rinjaye a cikinta. Kenan yanzu kotuna ba su da ikon rusa wannan majlisa kamar yadda aka bukata. Shugban na Masar ya kuma ba da umarnin sake gudanar da bincike akan shari'ar da ake wa hambarraren shugaba Husni Mubarak wanda a watan Yuli ake yanke wa hukuncin daurin rai da rai . To amma da dama daga cikin al'umar kasar sun soki wannan hukunci da cewa sassauci ne.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman