Murar tsuntsaye ta bulla a Kwango | Labarai | DW | 31.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Murar tsuntsaye ta bulla a Kwango

Kwararru sun tabbatar da samun sabon nau'in cutar masassarar tsuntsaye a kauyukan jamhuriyar Dimokuradiyyar kwango. Kauyukan dai na kan iyaka ne da kasar Yuganda wadda da ma ke da kwayar cutar tsuntsayen nau'in H5N8.

Rahotannin daga jamhuriyar Demokuradiyyar Kwangon na cewa an sami bullar cutar murar tsuntsayen ne nau'in H5, a garin Ituri da ke arewa maso gabashin kasar. Kwayoyin cutar da suka bulla a kauyuka 3 da ke yankin, hukumar kula da lafiyar dabbobi ta duniya ta ce babbar barazana ce ga musamman kaji.

Kauyukan dai na kan iyaka ne da kasar Yuganda wadda da ma ke da kwayar cutar tsuntsayen nau'in H5N8. Ba a dai yin cikakken bayani kan sabuwar kwayar cutar ta Kwango a yau ba.