Murƙushe masu zanga-zanga a Yukren ya harzuƙa ′yan adawa | Siyasa | DW | 02.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Murƙushe masu zanga-zanga a Yukren ya harzuƙa 'yan adawa

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta buƙaci bayanai daga mahukuntan Kiev sakamakon murƙushe masu zanga-zangar da 'yan sandan ƙasar suka yi

Masu adawa a ƙasar Ukraine sun cigaba da matsawa shugaban ƙasa Viktor Yanukovich lamba saboda matsayin gwamnatinsa kan shiga haɗin gwiwa da Turai. A yanzu haka dai masu adawar sun tare tituna, sun hana ma'aikatan gwamnati zuwa ofisoshinsu, sun kuma kafa tantuna a dandalin da suke zanga-zangar. A jiya lahadi sun yi ta bore har cikin dare lamarin da ya kai ga arangama da 'yan sanda inda har kusan mutane 150 suka yi rauni.

Ba kamar yadda aka yi tsammani ba wannan rikicin yana ƙara ta'azara musamman a ɓangaren 'yan adawa tun bayan da kafofin yaɗa labarai suka bada labarin cewa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi rauni lokacin boren ya cika a gadon asibiti. Masu zanga-zanga ƙalilan suka rage kan tituna wajenjen ƙarfe huɗu na asuba bayan da 'yan sanda suka riƙa fatattakarsu to sai dai da yawa na ganin wannan gwaji ne na ganin nisan da gwamnatin za ta yi wajen tabbatar da wannan aniyar ta ta, irin su Andreas Umland wani masanin kimiyyar siyasa a birnin Kiev.

Kujerar Victor Yanukovich na rawa

"Mahukuntan ƙasar sun shiga ruɗu a yanzu haka kuma babu dabarar da basu gwadawa dan ganin sun shawo kan wannan zanga-zangar dake cigaba da ta'azara, kuma wannan mataki ne wanda ya nuna cewa babu matakin da zai yi aiki a yanzu haka domin dama wannan abu ne da bai yi farin jini ba."

Protesters are seen near barricades which blocked the main avenue in Kiev December 2, 2013. About 1,000 protesters blocked off the Ukrainian government's main headquarters on Monday in protest at its decision to suspend moves to deepen integration with Europe and to revive economic ties with Russia. REUTERS/Vasily Fedosenko (UKRAINE - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Masu adawa da gwamnati

Abin da ke daɗa harzuƙa 'yan adawa shi ne ƙin rattaba hannun da shugaba Victor Yanukovich ya yi kan yarjejeniyar kasuwanci mara shinge da Turai bisa zargin matsain lamba daga Rasha, ita dai Rasha tana neman Ukraine ta kasance cikin ƙungiyar haɗin kan haraji na Turai da Asiya, wanda ke tsakanin ita Rashan da Kasakstan da Belarus, kuma shi yasa take ganin buɗe iyakar ta Ukraine wataƙila ya zama da haɗari.

Masana da dama dai na ganin cewa babban hatsarin shi ne mai yiwuwa wannan matakin da ya ɗauka yayi sanadiyyar barin sa muƙamin na shugaban ƙasa, kuma idan har aka yi haka 'yan adawa ne zasu girka gwamnatin wucin gadi, kuma akwai jamiyyu uku waɗanda suka haɗa da Batkishina da Udar da Svoboda waɗanda suka riga suka haɗa kansu waje guda.

Kyryl Savin shugaban gidauniyar Heinrich- Böll dake Kiev ya fayyace mana yadda jamiyyun siyasar ƙasar ke tasiri inda ya ce a wurinsa jagorar adawa shi ne Arsenji Jazenuk daga jamiyyar Batkivshina amma ba ɗan damben nan Klitschko kamar yadda kowa ke faɗa ba:

Matsayin 'yan adawa

"Bana tsammanin Klitchko madaugun adawa ne na haƙiƙa ba, domin ƙarfin siyasar shi da yawa idan aka kwatanta da na Batkivshina, kuma a ra'ayi na Klitcho ba ya saha'awar ɗaukar wani nauyi mai yawa, idan na muka yi la'akari da abin da ya faru ranar lahadi, yadda ko ɗaya bai kasance a wurin zanga-zangar ba domin jirginsa ya gaza sauka saboda hazo, sannan kuma ana gobe za a yi zanga-zangar ya tashi ya bar ƙasar babu zato babu tsammani yana mai cewa ya je wani taro ne a Hamburg"

Protesters are seen near barricades which blocked a street in Kiev December 2, 2013. About 1,000 protesters blocked off the Ukrainian government's main headquarters on Monday in protest at its decision to suspend moves to deepen integration with Europe and to revive economic ties with Russia. REUTERS/Vasily Fedosenko (UKRAINE - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)

Masu zanga-zanga kusa da shingaye

A yanzu dai lamarin ya zama tamkar ta reshe mai juyawa da mujiya, domin duk da cewa shugaba Yanukovich ba shi da hannu kai tsaye da murƙushe masu zanga-zanga, 'yan majalisa na barin jami'yyarsa domin rashin amincewa da shi. Sai dai Andreas Umland masanin kimiyyar siyasar dake birnin Kiev ya ce dole a tsaye wajen shawo kan wannan matsala

"Yana da mahimmancin gaske a ce an samar da maslahar da zata shafi shiyoyin siyasa domin kwantar da wannan rikicin na Ukraine, kuma ƙungiyar Tarayyar Turai tana da muhimmiyar rawar takawa, domin Turan babbar ƙawa ce ga Rasha a fanin cinakayya kuma za ta iya ɗaukar matakin da zai takurawa Rashar idan har tana so

A nata ɓangaren, Turai ta ce tana buƙatar bayyanai domin tana Allah wadai da yadda 'yan sanda ke tursasawa masu gudanar da zanga-zanga ta lumana.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu