Mummunar ambaliyar ruwa a Afirka ta halaka ɗaruruwan mutane | Labarai | DW | 15.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mummunar ambaliyar ruwa a Afirka ta halaka ɗaruruwan mutane

Jami´ai sun ce ambaliyar ruwa a fadin yammacin Afirka da kasashen kudu da Sahara ta yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 200 yayin da ta shafi sama da mutane miliyan daya. Akalla mutane dubu 260 suka rasa muhallinsu a kasar Ghana inda dubun dubatan gidaje da filayen noma suka lalace. A gabashin Afirka ma kasashen Ethiopia da Rwanda da kuma Uganda su ma ambaliyar ruwan ta yi musu ta´adi. A halin da ake ciki MDD na duba yiwuwar tura wata tawagar kwararru akan kula da bala´o´i.