Mummunan hali na ′yan gudun hijira a Turai | Labarai | DW | 13.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mummunan hali na 'yan gudun hijira a Turai

Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da samar da mafita ga kananan yara da ke neman mafaka a kan iyakar kasar Girka da Italiya.

Shugaban hukumar kare hakkin 'yan Adam a Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein, ya koka kan yadda 'yan gudun hijira ke shan azaba a kan iyakar kasashen Girka da Italiya. Shugaban ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake girke yara kanana a gidajen yarin da ke killace da wayoyi. Zeid Al Hussein ya kirayi hukumomi da su nemar wa yara kananan mafita a yayin da suke neman mafaka.

Zeid Ra'ad Al Hussein, ya kuma bukaci majalisar koli ta hukumar kare 'yancin dan Adam ta MDD da ta karfafa kiraye-kirayenta kan yadda ake cin zarafin 'yan gudun hijira a wasu kasashen Turai. 'Yan gudun hijirar Iraki da Siriya na jibge a kan iyakokin kasashen Turai tun bayan da EU ta cimma yarjejniya da Turkiyya, wacce ta tanadi mayar da su inda suka fito.