Mummunan fada ya barke a Bangui | Labarai | DW | 13.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mummunan fada ya barke a Bangui

A jamhuriyar Afirka ta Tsakiya an ji karan manyan makamai a anguwar PK 5 da ke zama matattara ta Muslmi a kasar

A ranar Lahadin nan al'ummar kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kada kuri'arsu a kuri'ar raba gardama da za ta kai ga yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar, abin da ake ganin cewa na da muhimmiyar rawa da zai taka a kokari na kawo karshen yaki da kasar ke ciki tsawon shekaru uku. Tuni dai 'yan tawaye suka yi fatali da wannan shiri inda suka bukaci a kafa sabuwar gwamntin riko a kasar.

An dai ji karar bindigogi da makaman roka a unguwar PK 5 da ke zama matattara ta Muslmi a kasar abin da ya sanya dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya suka kai wa jam'a da ke jefa kuri'ar dauki a makarantun da ake wannan zabe.

Amincewa da sabon kundin tsarin mulki dai a kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zai sanya a ranar 27 ga watannan na Disamba ayi zaben shugaban kasa da ma na 'yan majalisar dokoki, a kokarin da ake yi na sake mai da kasar bisa turba ta dimokradiya.

Rikici dai mai nasaba da addini tsakanin 'yan Seleka da Anti Balaka a wannan kasa ya sanya kisan dubban mutane, yayin da kusan miliyan suka kaurace wa muhallansu.