Muhimmancin yanar gizo ga daliban Afurka a Jamus | Siyasa | DW | 26.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Muhimmancin yanar gizo ga daliban Afurka a Jamus

Dalibai da 'yan ci rani daga kasashen Afurka na amfani da yanar gizo don tuntubar juna a duk fadin Jamus

A cikin shekarun baya-bayan nan manufar amfani da yanar gizon ta dada samun muhimmanci tsakanin dalibai da ma ‘yan ci rani daga nahiyar Afurka dake zaune a nan Jamus. Misali dalibai daga kasar Tanzaniya su kan yi amfani da wani kamfani mai suna klimanjaro.de domin tuntubar juna ta adreshin E-Mail. Wani dalibi dan kasar Tanzaniya mai suna Harold Ishebabi da DW ta tuntube shi cewa yayi, yau kimanin shekaru tara ke nan da shigo nan kasar domin nazarin fasahar lantarki a garin Kaiserslautern. Kuma da farkon fari ya sha fama da wahala wajen koyan Jamusanci da al’adun al’umar kasar da dai sauran matsalolin da dalibai suka saba fuskanta wajen neman karin ilimi a jami’a. Ya ce dukkan wadannan abubuwa na tattare a zuciyarsa ba kuma wanda zai yi musayar ra’ayi da shi, har ya zuwa lokacin da ya sadu da wata ‘yar kasarsu ta Tanzaniya, wadda ita ma ta fuskanci matsaloli irin shigen nasa. Nan take suka tsayar da wata muhimmiyar shawara, in ji Harold Ishebabi, wanda ya ci gaba da cewar:

“”Da farko dai maganar dake akwai ita ce, a wancan lokaci mutun zai hadu da wani dan uwansa daga Tanzania, amma ba su san juna ba. A sakamakon haka dukkansu ke fama da kadaici. Ana kan haka na sadu da wannan matar na kuma gano cewar akwai ‘yan kasar Tanzaniya da dama a nan Jamus. Nan take ra’ayi ya zo mana na kafa wata kungiya ta hada ka, wadda zata ba mu wata dama ta kyautata sadarwa tsakaninmu ta yanar gizo yadda zamu iya tuntubar juna akai-akai a duk fadin Jamus.”

Ba da wata-wata ba muka tashi gadan-gadan wajen ganin cewar wannan shawara ta tabbata kuma ba da dadewa ba muka kirkiro shafinmu na klimanjaro.de, domin zama wata kafa ta sadarwa ta hanyar E-Mail ta yadda dukkan ‘yan kasar Tanzaniya zasu iya musayar ra’ayoyi tsakaninsu a duk fadin Jamus. Yau dai kimanin shekaru shida ke nan da kirkiro wannan shafi na yanar gizo kuma wasu daruruwan ‘yan Tanzaniya dake nan Jamus suna amfani da shi domin tuntubar juna.

“Wannan wata muhimmiyar kafa ce garemu. Idan a matsayinka na dalibi kana fama da wasu matsaloli zaka iya samun mai ba ka shawara da wasu ra’ayoyi da dama domin tinkarar matsalolinka. Wannan abu yana da muhimmanci, saboda daliban Tanzaniya sun barbazu ne a sassa daban-daban kuma mutum zai samu shawara kusan daga kowane bangare.”