Muhawarar sake fasalin Najeriya na kara zafi | Siyasa | DW | 24.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Muhawarar sake fasalin Najeriya na kara zafi

A Najeriya batun sake wa kasar fasali na kara daukan hankali a dai dai lokacin da gwamnatin kasar ta ce shugaban Najeriyar baya da karfin ikon yin hakan duk da matsin lamba da ‘yan siyasa da shugabanin alumma ke yi.

Batun sakewa Najeriya fasali da sannun a hankali ke kara amo a fagen siyasar Najeriyar inda shugabanin al'umma da masu kokarin kaiwa ga madafan iko musamman daga yankin kudancin kasar ke kara matsin lamba na lallai sai a yi hakan, a matsayin hanya ta karshe ta kaiwa ga samun mafita.

Matsin lamba da kokari na tursasawa gwamnatin don ganin ta bada bori kai ya hau a kan wannan lamari ya sanya gwamnati fitowa fili ta ce ba ta fa da ikon yin haka domin batu ne na majalisun dokoki saboda sai an taba dokar kasa kafin yin haka. Masu sharhi dai na ganin wadanda suka matsa kan wannan batu suna da wata manufa ce.

Sai dai ga mafi yawan ‘yan yankin Kudancin Najeriya na masu bayyana cewa sake fasalin Najeriyar ce fa mafita guda ta samun zaman lafiya da dorewar Najeriyar a matsayin kasa daya al'umma daya. Janaral Ike Nwachukwu na cikin masu wannan ra'ayi da ya kaisu gudanar da taro na musamman a kan batun.

Amma shin me tsarin mulkin Najeriyar ya ce ne a game da wannan batu? Barrister Zubairu Namama lauya ne mai zaman kansa da ke Abuja ya ce 'yan Najeriya ne ke da hakki kan irin wannan batu kuma za su tunkari majalisa ne kawai.

Ga ministan kula da harkokin matasa da wasani Solomon Dalung na ganin tone-tonen da ake yin na da manufa. A yayin da ake laluben mafitar ga wannan al'amari.

Da alamun kallo ya koma ga ‘yan majalisun dokokin Najeriyar a kan wannan batu da a fili zai ci gaba da mamaye fagen siyasar Najeriyar da ma yakin neman zaben 2019 da wasu ke ganin shi ne ma dalilin bude wuta a kan lamarin.

Sauti da bidiyo akan labarin