Taron Global Media Forum a Turance karo na 12 wanda tashar DW ta dauki nauyin ya mayar tafka zafafan muhadarori a taron. Taken taron na bana shi ne sauyin madafan iko.
Tun farko lokacin bude zaman taron Peter Limbourg shugaban tashar ta DW, da kuma Frank-Walter Steinmeier shugaban kasar Jamus, sun yi magana kan batutuwa dabam-dabam kama daga zaben 'yan majalisar Tarayyar Turai, da batun ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai, da sauyin yanayi da sauransu.