Muhawara kan hare-haren ta′addanci a Nijar | Siyasa | DW | 29.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Muhawara kan hare-haren ta'addanci a Nijar

Bangarori daban-daban na Jamhuriyar Nijar na tofa albarkacin bakinsu kan kamarin hare- haren ta'addanci da ke addabar yankuna da ke kan iyakokin kasar duk da matakin da gwamnati ke dauka ciki har da dokar ta-baci.

Harin baya-bayan nan ya abku ne a jihar Terra mai makwabtaka da Burkina Faso inda 'yan ta'adda suka afka wa jam'ian tsaron Nijar tare da halaka uku da jima wasu da dama rauni. Sai dai abin da ke daukar hankalin masu sharhi shi ne, hare-haren na faruwa ne yayin da yankin ke cikin dokar ta-baci. Majalisar dokoki ce ta amince da dokar a farkon watan Maris har na tsawon watanni uku a wani yunkuri na dakile matsalar ta yawaitar hare-haren da hukumomin kasar suke kyautata zaton na fitowa ne daga arewacin Mali.

Sai dai Alhaji Idi Abdou wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum kuma dan kungiyoyin farar hulla  ya ce " idan muna son samun lafiya a Tillabery sai kasarmu ta yi kokuwa yanda za'a je tare da kasashen da ke cikin matsalar a fatattakesu a tungarsu da ke Mali."

Niger Flüchtlinge aus Nigeria (DW/A. Cascais
)

'Yan gudun hijira sun yawaita sakamakon hare-hare a Nijar

Hare-haren 'yan ta'addan na kuma faruwa ne a yayin da rundunonin sojojin kasashen ketare kamar su Barkhane na Faransa da na Amirka ke girke a kasar ta Nijar da ma sauran kasashe makwabta don yaki da 'yan ta'adda a yankin Sahel. Sai dai shugaban kwamitin tsaro na majalisar Dokokin Nijar Hama Assah ya ce "  A Burkina da Mali da Chadi da Nijar da Najeriya duk kamata yayi mutane su bayar da hadin kai a bakin iyakokin kasashen nan domin abin ba zai kare ba idan babu hadin kai."

Jamhuriyar Nijar dai na fama da matsalolin kai hare-haren a daukacin iyakokin kasar da  Najeriya da Libiya da Mali, duk da matakan da gwamnatin kasar ta ke dauka na kashe akalla kashi 10 % na kasasfin kudin kasar a fannin kare kasa da sayen makamai.

Sauti da bidiyo akan labarin