1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhammadu Buhari ya gana da Jacob Zuma

Ubale Musa/ASMarch 8, 2016

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da takwaransa na Afirka ta Kudu Jacob Zamu a wani zama da suka yi a Abuja.

https://p.dw.com/p/1I9NG
Äthiopien Gipfel Afrikanische Union - Muhammadu Buhari & Jacob Zuma
Buhari da Zuma na son a bawa Afirka kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinki DuniyaHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Yayin ganawar da suka yi dai shugabannin kasashen biyu sun ratttaba hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi har guda 30 da ke da burin habbaka harkokin tattalin arziki da tsaro da yaki da fataucin muggan kwayoyi da kariya ga tekun Gini. Shugaban Afirka ta Kudu Jacob zuma ya ce tattaunawar da suka yi da ma amincewa kan batutuwa da dama sun bude sabon babi na kyautatuwar danganta tsakanin kasashen.

Kafin shekara ta 1999 kamfanonin Afrika ta Kudu Hudu kawai ke harkoki na kasuwanci a cikin tarrayar Najeriya to sai dai daga bisani abubuwan sun sauya sosai. Ya zuwa yanzu kamfanoni sama da 120 da suka hada da sadarwa da gidaje da manyan shagunan ciniki ne ke harkokinsu cikin kasar ta Najeriya. Sannan kuma dubban 'yan Nigeria ne ke ziyartar kasar ta Afirka ta Kudu don huldodi da suka danganci kasuwanci da sauran batutuwa.

To sai dai a dan tsakanin nan, wani batu da ya nemi mamaye bakuna na bangarorin biyu dai na zaman makomar wata tarar Naira miliyan Dubu 780 din da Najeriya ta kakabawa kamfanin sadarwa na MTN. A share guda kuma ra'ayin shugabannin biyu ya daidaita bisa bukatar samar da kujerar dindin ga nahiyar Afirka a kwamitin tsaro na Majalisar Dinki Duniya inda suka ce lokaci ya yi da Afirka za ta samu kujera duba da yawan al'umma da nahiyar ke da ita.