Mugabe ya nemi a bashi kariya a Zimbabuwe | Labarai | DW | 23.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mugabe ya nemi a bashi kariya a Zimbabuwe

Majiya daga bangaren gwamnatin Zimbabuwe ta bayyana cewa Mugabe dan shekaru 93 ya fadawa masu shiga tsakanin cewa ya na so ya mutu a kasar ta Zimbabuwe ba shi da wani buri na barin kasar don neman mafakar siyasa.

Tsohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ya samu tabbaci na cewa ba za a gurfanar da shi gaban kuliya ba kuma zai samu tsaro na lafiyarsa a kasarsa ta haihuwa a wani bangare na yarjejeniyar da aka kulla da shi kafin ya mika takardar ajiye mukamin shugabancin kasar kamar yadda wata majiya da ke kusa da wadanda suka shirya yarjejeniyar ta nunar a wannan rana ta Alhamis.

Majiyar daga bangaren gwamnatin Zimbabuwe ta bayyana cewa Mugabe dan shekaru 93 ya fadawa masu shiga tsakanin cewa ya na so ya mutu a kasar ta Zimbabuwe ba shi da wani buri na barin kasar don neman mafakar siyasa.

A cewar majiyar da ba ta so a bayyanata ba, Mugabe ya yi jawabin nasa a yanayi na kada zuciya kuma ya ce daukar matakin ya zame masa dole ne. A gobe Juma'a ne dai ake sa ran za a rantsar da Emmerson Mnangagwa mataimaki da Mugabe ya kora da kuma ya koma gida a ranar Laraba.