Mugabe ya ba AU tallafin Dala miliyan daya | Labarai | DW | 03.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mugabe ya ba AU tallafin Dala miliyan daya

A wani mataki na taimakawa kungiyar AU zama da gindinta, shugaban Zimbabuwe Robert MUgabe ya baiwa kungiyar gudunmawar kudi dala miliyan daya.

Shugaban kungiyar gamaiyar Afirka Moussa Faki ya soki kasashe mambobin kungiyar dangane da rashin nuna goyon baya ga takwarorinsu da ke fuskantar annobar fari.

Yana magana ne a taron kolin shugabanin kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Taron kolin kungiyar yana kuma duba yadda za'a yiwa kungiyar garanbawul ta zamo mai dogaro da kanta wajen samun kudade maimakon mika kokon bara ga kasashen yamma.

A waje guda dai shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe ya bada gudunmawar dala miliyan daya ga kungiyar ta AU tare da fatan sanya dan ba abin koyi ga sauran shugabanni.

Tsawon shekaru 60 kungiyar ta gamaiyar Afirka na dogaro ne da gudunmawar jin kai daga Kungiyar tarayyar Turai da Bankin Duniya.