1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe na shan suka kan mukamin WHO

Yusuf Bala Nayaya
October 21, 2017

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na ci gaba da sukar matakin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na ba wa Shugaba Robert Mugabe jakadanta na lafiya a duniya.

https://p.dw.com/p/2mI0U
Simbabwe Präsident Robert Mugabe
Hoto: Reuters/P. Bulawayo

Babban daraktan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana bada wannan mukami a babban taron yaki da cutattuka da ba sa bazuwa (NCDs) a Yurugai ranar Laraba. Shugaba Mugabe mai shekaru 93 a duniya da kasashen Yammacin duniya da 'yan kasarsa ke tuhuma kan lalata harkokin lafiya a kasarsa, da take hakkin bil Adama a cewar Iain Levine, mataimakin darakta a kungiyar Human Rights Watch, ba shi wannan mukami da ya cancanci mutane da suka yi fice a tallafin al'umma abin kunya ne.

Mai magana da yawun Hukumar Lafiyar ta Duniya kuwa Christian Lindmeier ya ce shugaban hukumarsu na bukatar masu fada a ji ne a harkokin kula da lafiya da hukumar ta sa a gaba. Jami'an diflomasiya dai daga Yammacin Duniya sun sha mamaki na bayyana sunan na Mugabe cikin jagororin wannan tafiya ta wayar da kan al'umma kan wadannan cutattuka da ba a baza su.