Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin za a ji cewa a yankin Tigray na kasar Habasha a iya cewa tsugunne tashi ba ta kare ba inda wutar rikici a yankin ke kara ruruwa duk da janyewar da sojin gwamnati suka yi.
Dakarun kasar Sudan suna tuhumar sojojin Habasha da kashe jami'an tsaronsu guda bakwai da farar hula daya, wadan da aka kashe suna cikin mutanen da aka yi garkuwa da su.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya shirya wani zama domin nazarin halin da ake ciki game da rikicin kasar Ethiopia da mayaka masu neman 'yancin yankin Tigray.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci gwamnatin Habasha tatabbatar kungiyoyin agaji jinkai sun kai yankin Tigray mai fama da rikici.
'Yan tawayen da ke yaki da gwamnatin Habasha sun yi watsi da rahotannin cewa za su haifar da "zubar da jini" idan suka shiga birnin Adis Ababa, duk da cewa dubban mutane sun yi gangamin marawa sojoji baya a Addis Ababa.