Ana zaben shugaban kasa
October 15, 2019Masu sharhi kan lamuran siyasa na ganin cewa duk da farin jinin jam'iyyar adawa ta Renamo, da wuya ta iya kayar da Jam'iyyar mai ci ta Frelimo da ta mulki kasar tun bayan da ta sami 'yanci kai a shekarar alifa da dari tara da saba'in da biyar (1975) Shugaba Filipe Nyusi dan shekaru sittin da haihuwa na fatan yin tazarce a wa'adi na biyu da zai ba shi damar mulki na wasu shekaru biyar.
Kasar da ke farfadowa daga iftala'in guguwa da ta raba kusan miliyan biyu da muhallinsu na fama da hare-hare 'yan bindiga musanman a yankin Arewacin kasar, wanda ya haifar da tarnaki a kokarin gwamnati na da gudanar da ayyukan raya kasa. Mutum akalla miliyan goma sha uku aka yi wa rejista don kada kuri'a wanannan zaben na yau. Daga karfe bakwai na safe a gogon kasar za a bude rumfunar zaben ana kuma sa ran jin sakamakon zaben a ranar Alhamis mai zuwa.