Moroko:Mutum 15 sun mutu a turmutsitsi | Labarai | DW | 19.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Moroko:Mutum 15 sun mutu a turmutsitsi

A kasar Moroko mutane akalla goma sha biyar ne suka mutu yayin da wasu biyar suka sami rauni a turmutsitsin da aka samu a lokacin da ake rabon agajin abinci.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ce ta sanar da faruwar lamarin inda ta ce an soma gudanar da bincike don sanin musababin aukuwar yamutsin a wannan yankin kasar da ke fama da tsananin talauci.Wani shedan gani da ido ya ce lamarin ya auku ne a yayin da daruruwan mata da suka hadu a harabar gidan wani attajiri da ya saba rabon kayan abinci ke rige-rigen karbar kayan abincin.