Morales ya lashe zabe a Bolibiya | Labarai | DW | 13.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Morales ya lashe zabe a Bolibiya

Shugaban kasar Bolibiya Evo Morales ya sake lashe zaben shugaban kasar wanda ya bashi damar darewa kan karagar mulki a karo na uku.

A zaben da ya gudana Morales ya samu kaso 60 cikin 100, inda abokin takararsa Samuel Doria Medina ya samu kaso 25 na kuri'un da aka kada. Masu fashin baki na ganin Morales ya lashe wannan zaben ne biyo bayan nasarar da ya samu wajen tabbatar da bunkasar tattalin arzikin kasar ta Bolibiya, abun da mafi akasarin kasashen yankin Latin Amirka suka gaza samu. A jawabin da ya yi na samun nasara Morales da ke da kimanin shekaru 55 a duniya, ya ce Bolibiya za ta ci gaba da bunkasa haka nan kuma zai tabbatar da ganin sun kara samun daidaito a fannin tattalin arzikin kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo