1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gidauniyar Mo Ibrahim ta karrama Issoufou Mahamadou

Abdoulaye Mamane Amadou
March 8, 2021

Gidauniyar Mo Ibrahim ta bai wa shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou lambar yabo bisa jan kokarinsa na karfafa tsarin dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3qMQr
Niger Symbolbild Fahne | Mahamadou Issoufou
Hoto: Boureima Hama/AFP

Duk da kasancewar shi jagoran shugaban daya daga cikin kasar da ta fi kowace kasa talauci a duniya, shugaba Issoufou ya bayyana kyautar a matsayin wani ci gaba, da kuma kwarin gwiwar bayar da gudunmawa wajen bunkasa tsarin dimukuradiyya da kyakyawan jagoranci a Nijar da Afirka har ma da duniya baki daya. Shugaba Issoufou ne zai kasance na shida kenan da ke samun kyautar gidauniyar, wacce tun bayan shekarar 2017 da aka kasa samun wani daga cikin tsoffin shugaban kasashen Afirka da suka cika shardin da aka gindaya.

Duk da matsayin da yake da shi, shugaban Nijar Mista Issoufou ya ki ya sauya kundin tsarin mulki don ci gaba da tafiyar da iko, tare da shirya zaben da hukumar CENI ta ayyana Mohamed Bazoum a matsayin wanda yayi nasara, duk da yake madugun 'yan adawar kasar Mahamane Ousmane ya kalubalanci sakamakon tare da garzayawa zuwa kotu.