1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mnangagwa: Zimbabuwe za ta shirya sahihin zabe

Salissou Boukari
January 19, 2018

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya ce ya na bukatar a samu halartar baki 'yan kallo na kasashen waje a zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokoki da za a yi a kasar cikin wannan shekara.

https://p.dw.com/p/2r9pR
Simbabwe Harare Vereidigung Präsident Emmerson Mnangagwa
Shugaban Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa lokacin da ya yi rantsuwar kama aikiHoto: Reuters/M. Hutchings

Mnangagwa ya yi wannan tsokaci ne a wata hira da aka yi da shi ta jaridar Financial Times, inda ya ce abun da suke bukata shi ne zabe na gaskiya wanda zai yi kima a idanun duniya, don haka yana son Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai su turo da 'yan kallonsu a zabukan kasar masu zuwa.

Yayin wata ziyara ce dai da ya kai a kasar Mozambique a ranar Alhamis a wani rangadi da ya soma a kasashen yankin, Shugaban na Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya sanar cewa zabukan kasar za su wakana ne cikin watanni hudu zuwa biyar masu zuwa, inda ya ce zai yi duk abun da ya dace na ganin an yi zabe na gaskiya mai kima.