1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mnangagwa ya yi watsi da gwamnatin hadaka

Zulaiha Abubakar
January 5, 2018

Shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabuwe yayi watsi da batun kafa Gwamnatin hadaka a kasar jim kadan bayan ya ziyarci madugun adawa Morgan Tsvangirai a Wannnan Jumma'a .

https://p.dw.com/p/2qOtp
Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabuwe
Shugaba Emmerson Mnangagwa na ZimbabuweHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Wannan mataki na shugaba Emmerson Mnangagwa na kasar Zimbabuwe ya saba da alkawarin da ya yi bayan da guguwar sauyi ta yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, inda ya ce Zimbabuwe na bukatar gudunmawar 'yan adawa da masu zuba jari don ta tsaya a kan kafafunta. Mr Mnangagwa ya shaida wa manema labarai cewar babu fa'idar yin hadakar gwamnati a halin yanzu tsakanin jam'iyyarsa ta ZANU-PF da kuma ta adawa wato MDC da a baya suka yi tafiya tare har i zuwa shekara ta 2013 lokacin da aka yi ta samun rikicin shugabanci a cikin jam'iyyun.

A share guda Morgan Tsvangirai, wanda zai kara da Mnangagwa a zaben mai zuwa yana karbar magani sakamakon jinyar da yake yi tun shekara ta 2016, koda yake ya bayyana cewar lafiyarsa ta inganta.