Misirawa na jiran sakamakon zabe | Labarai | DW | 25.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Misirawa na jiran sakamakon zabe

Hukumomi a kasar Masar sun bayyana cewa, a yammacin yau Talata za su sanar da sakamakon kuri'ar raba gardama da aka kada

Egyptian election workers empty a ballot box for counting at the end of the second round of a referendum on a disputed constitution drafted by Islamist supporters of president Mohammed Morsi at a polling station in Giza, Egypt, Saturday, Dec. 22, 2012. Egypt's Islamist-backed constitution headed toward likely approval in a final round of voting on Saturday, but the deep divisions it has opened up threaten to fuel continued turmoil. (Foto:Nasser Nasser/AP/dapd)

Wajen tara kuri'un raba gardama da aka yi a Masar

A kasar Masar yaune ake saran sanar da sakamakon kuri'ar raba gardama. Alkalai sun jinkirta sanar da sakamakon bayan da masu adawa suka yi zargin magudi, inda yanzu ake gudanar da bincike kafin a fitar sakamakon a hukumance. Kundin tsarin mulkin dai masu kaifin kishin Islama dake dasawa da shugaba Muhammad Mursi ne suka rubuta shi. Inda tuni kungiyar Muslem Brotherhood ta sanar da cewa kashi 64 cikin dari na wadanda suka kada kuri'a sun amince da sabon kundin tsarinmulkin. Idan dai aka amince da sabon kundin tsarin mulkin a hukumance, to za a gudanar da zaben yan majalisar dokoki nan da watanni biyu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Saleh Umar Saleh