Ministocin kasashen Rasha da Turkiyya sun gana | Labarai | DW | 03.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ministocin kasashen Rasha da Turkiyya sun gana

A Karo na farko tun bayan kakkabo jirgin saman kasar Rasha da Turkiyya ta yi ranar 24 ga watan Nowamba, ministocin harakokin waje na kasashen biyu sun gana a wannan Alhamis.

A karo na farko tun bayan rikicin diplomasiyyar da ya barke tsakanin kasashen Rasha da Turkiyya biyo bayan harbo jirgin saman kasar Rasha da Turkiyyar ta yi, an gana a wannan Alhamis tsakanin ministocin harakokin wajen kasashen biyu a birnin Belgrade daura da taron hukumar tsaro da kyautatuwar hulda a tsakanin kasashen Turai ta OSCE da ya gudana a wannan Alhamis a babban birnin kasar ta Sabiya .

Wata majiyar diplomasiyya da ta so a sakaya sunanta ta kwarmata wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa ministocin biyu sun yi ganawa ta tsawon mintoci 40, sai dai ba bu wani bayani dangane da batutuwan da suka tattauna a kai.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen na Rasha da Turkiyya tun bayan da kasar Turkiyyar ta kakkabo wani jirgin saman Rasha a kan iyakarta da kasar Siriya a ranar 24 ga watan Nowambar daya gabata.