1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministar tsaron Jamus ta yi murabus

January 16, 2023

A wannan Litinin din ce ministar tsaron Jamus Christine Lambrecht ta sanar da yin murabus a hukumance.

https://p.dw.com/p/4MFW2
Ministar tsaron Jamus Christine Lambrecht
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Matakin ajiye aikin Christine Lambrecht na zuwa ne, bayan da kafofin yada labarai suka sanar a ranar Juma'ar da ta gabata cewa ministar na shirin ajiye aiki sakamakon mummunar sukar da ta ke sha kan sakonta na sabuwar shekara. A sakon ta na sabuwar shekara, Lambrecht ta yi magane dangane da yakin Ukraine yayin da ake tsaka da wasan wuta.

Mambobin kungiyar CDU sun yi watsi da kiraye-kiraye kan ta yi murabus. Dama dai an dade ana rade-radin cewa ministar ka iya ajiye aiki. Lambrecht ta kuma sha yin suka ga gwamnatin Jamus, kan jan kafar da ta ke yi wajen turawa Ukraine manyan makamai.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na fatan nada sabon minista da zai maye gurbin Lambrecht a nan gaba. Tuni kuma aka mika jerin sunayen wadanda za a tantance, domin zaben sabon minista gaban majalisar dokokin kasar.