1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus tabi sahun takwarorin ta game da batun muhalli

Zulaiha Abubakar
October 10, 2018

Ministar muhalli na Jamus Svenja Schulze ta bayyana gamsuwa da yarjejeniyar da takwarorinta na kungiyar tarayyar Turai suka cimma kan rage kashi 35 na hayakin da ke fita daga motoci a shekara ta 2030.

https://p.dw.com/p/36IQ6
Svenja Schulze SPD Wissenschaftsministerin NRW
Hoto: picture alliance/dpa

Ta kara da cewar wannan mataki wani ci gaba ne  idan akayi la'akari da irin cutarwa da hayakin ababan hawa ke yi wa muhalli,wannan bukata dai na daga cikin kudirorin da shugabannin kasashen duniya suka sanya a gaba yayin wani taron sauyin yanayi da ya gudana a birnin Paris tun a shekara ta 2015 .