1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministar ilimin Jamus ta ajiye aikinta

February 9, 2013

Annette Schavan ta yi murabus daga mukaminta na ministar ilimi sakamakon zarginta da amfani da litattafan wasu ba bisa ƙaida ba.

https://p.dw.com/p/17bTe
Hoto: Reuters

A wannan asabar ɗin ce Annette Schavan tayi murabus, sakamakon samunta da laifin amfani da ayyukan mutane ba tare da ta rubuta sunayensu ba lokacin da ta yi karatun samun dokta a jami'a. Ranar talatar da ta gabata wata hukuma ta musamman ta sami ministar da laifin abun da ta kira yin zamba da gangan bayan da ta yi amfani da ayyukan wasu a littafin kammala karatun da ta rubuta shekaru 33 da suka gabata.

A wata ganawar haɗin gwuiwa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Annette Schavan suka yi da manema labarai, Merkel ta ce tana takaicin karɓar takardar murabus ɗin ministan, kuma ta yaba da ayyukan da ta yi a fagen siyasa na tsawon shekaru 17 yanzu:

Ta ce: " Na yi nadaman amincewa da wannan murabus saboda Annette Schavan mace ce sananniya kuma ƙwararriya sosai a fanin illimi da kimiyar siyasa a ƙasar mu, saboda irin ficcen da ta yi da kuma ƙwarewar da take da shi, zan ce gwamnatinmu ta yi babban rashi da wannan tafiyar na ta."

Yanzu haka dai ministar kimiyya ta jihar Niedersachsen Johanna Wanka ce zata maye gurbin Annette Schavan, a matsayin ministar kula da harkokin ilimi na tarayyar Jamus.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita : Zainab Mohammed Abubakar