1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mike Pompeo na ziyara a Saudiyya

Usman Shehu Usman
April 28, 2018

Sabon sakataren harkokin wajen Amirkan ya isa Riyad babban birnin kasar Saudiyya wannan dai ita ce ziyarar farko a matsayinsa na sakataren harkokin waje inda ya zabi kasar ta kasance kasar da zai ziyarta a fara aikinsa.

https://p.dw.com/p/2wrFM

  Ziyarar Pompeo a Saudiyya na da daukar hakali ta fannoni masu yawa, kama daga rikicin Siriya da Yeman, sai kuma uwa uba yadda gwamnatin Trump ke ingiza kiyayya kan Iran daga makobtanta. inda Trump ya sanar da ranar 12 ga watan gobe a matsayin ranr da zai bayyana mataki da matsayinsa kan yarjejeniyar nukiliyar Iran. Yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma da Iran, wace kuma Donald Trump ke matukar sukar lamarin. Daga kasar Saudiyya, sabon sakataren harkokin wajen na Amirka zai zarce Isra'ila da Jordan.