1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiki-kaka a Siyasar Jamhuriyar Nijar

Abdoulaye Mamman Amadou / LMJDecember 16, 2015

A Jamhuriyar Nijer hukumomin kasar sun sanar da ranar 21 ga watan Disamban nan da muke ciki a matsayin ranar da 'yan takara a zabukan kasar da ke tafe damar mika takardunsu ga hukumomin shari’a.

https://p.dw.com/p/1HOMm
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Sai dai matakin da majalisar ministocin kasar ta dauka na zuwa ne a yayin da ake cikin kiki-kaka kan batun kundin rijistar sunayen masu zabe da har yanzu ba a mika shi ga hukumomin kasar ba. Kundin tsarin mulkin Nijar sashe na 48 ya tilastawa gwamnatin yin zama na musamman domin daukar matakin, wanda gwamnatin ta ce ta yi shi ne bisa wani jadawali da hukumar zabe mai zaman kanta ta gabatar mata a ranar 20 ga watan Yulin da ya gabata.


Tankiyar gwamnati da 'yan adawa


Sai dai wani hanzarin ba gudu ba shi ne ana kiran taron ne a yayin da a hannu guda kura da hayaniya ke ci gaba da tashi tsakanin 'yan adawa da bangaren gwamnati dangane da kundin rijistar sunayen masu zabe da 'yan adawar kasar suka ce ya barsu cikin mamaki. Alhaji Doudou Mouhamadou shi ne kakakin kawancen adawa na FPR.

'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar
'Yan adawa a Jamhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta


Ya ce: "Ba a taba gabatar da kira ba a yayin da aka san abin da aka kira ba shi da tsari da alfanu, a kasar nan ba a taba shirya zabe mai kama da wannan ba mai rikici, kuma ba a taba ganin kasar da gwamnati ke cewa ta na tilastawa mutane yanda take so ko yanda taga dama da abin da 'yan Nijar basa so. Ba ya yiwuwa a haka rikici na siyasa mu ne bama so amma gwamantin kasar nan ta na matsa mana da dole sai mun yi, wanda kuma a ganinmu ba zai gadar da alkhairi ba."


Gwamnatin dai na zargin 'yan adawar kasar ne da neman tayar da zaune tsaye ta hanyar shirya hayaniya domin ganin hukumomi sun kasa shirya zaben a lokuttan da aka kayyade, Inji kakakin gwamnatin kasar Marou Amadou:

Zargin haddasa rikici


"Ina son in shaidawa kowa da kowa da karfin Allah a ranar 21 ga watan Fabarairu za a gudanar da zabubbukan shugaban kasa hade da na 'yan majalisar dokoki, domin mun lura cewar wannan hayaniyar da ake ta ta'allaka ne zuwa ga tursasa kasar shiga cikin wani mawuyacin hali na rashin shirya zabe, idan ba haka ba kun ce baku yarda da kundin zabe ba a shirya bincike sunayen masu zabe mun amince an fara kuma daga bisani sai wani can ya fito ya ce bai yarda da hakan ba? To ina mai tabbatar da cewar akwatunan zabe za su kasance a bude ranar nan saboda hakan duk wani mai shakku ko mai hasashen cewar ba a zaben to ya ma canza tunani."

Alhaji Saini Oumarou shugaban jam'iyar adawa ta MNSD Nasara
Alhaji Saini Oumarou shugaban jam'iyar adawa ta MNSD NasaraHoto: DW/M. Kanta

Kalamun dai na kakakin gwamantin kasar ya zowa 'yan adawar a karkace musamman ma zargin na su da cewar ba su da niyyar tafiya zabubuka. Kakakin 'yan adawa Alhaji Muhammadu cewa ya yi batun ba haka yake ba.