1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MH370: Bincike ya tabbatar da gano bangaren jikinsa

Suleiman BabayoAugust 5, 2015

Kwararru a birnin Toulouse na kasar Faransa sun tantance tarkacen jirgin saman da aka tsinta wanda ya tabbata ya fito daga jirgin saman Malesiya da ya bace.

https://p.dw.com/p/1GAmL
Frankreich Untersuchung Wrackteil MH370 Luftfahrttechnikzentrum bei Toulouse
Hoto: Reuters/Str

Firaminista Rajib Nazak na kasar Malesiya ya tabbatar da cewa tarkacen jirgin saman da aka tsinta wanda ya tabbata ya fito daga jirgin saman MH370. Kwararru masu bincike kan hadarin jiragen sama daga kasashe Faransa, da Amirka, da China, da Osteraliya, gami da Malesiya suka tantance bangaren jirgin sama da aka samu, da firaministan ya tabbatar ya fito daga jirgin saman kasar Malesiya na Boeing 777 mai lambar tafiya MH370, wanda ya bace fiye da shekara guda da ta gabata.

A makon jiya aka tsinci bangaren fikafikin jirgin saman a tsibirin Reunion da ke karkashin ikon Faransa, kusan kilo-mita 3000 daga wajen da ake tsammani jirgin saman ya fadi.

Masanan a birnin Toulouse suka yi gagarumin aikin tantancewar, abin da ya ba da haske bisa sanin makomar mutane 239 da ke cikin jirgin wanda ya yi batan dabo daga birnin Kuala Lumpur na Malesiya a kan hanyar zuwa birnin Beijing na kasar China cikin watan Maris na shekarar da ta gabata ta 2014. Tuni Firamnista Razak na Malesiya ya mika sakon ta'azi kan wadanda suke cikin jirgin saman.