MH17 - ana gudanar da bincike a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 21.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MH17 - ana gudanar da bincike a gabashin Ukraine

Vladimir Putin ya ba da tabbacin cikakken hadin kai a binciken faduwar jirgin saman Malaysia a yankin kasar Ukraine.

Tawagar masu bincike na kasar Holland sun fara gudanar da bincike a kan gawarwakin fasinjojin da ke cikin jirgin saman Malaysia nan MH17 da ya fadi a gabashin Ukraine. Sai dai suna aikin ne karkashin sa idon 'yan aware da ke goyon bayan Rasha. Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi kira ga 'yan awaren da su kyale kwararrun na kasa da kasa shiga wurin da jirgin ya fadi sannan su tabbatar da tsaron lafiyarsu. Putin din dai ya yi wannan kira ne bisa matsin lamba daga kasashen yamma na ya nuna ikonsa a kan 'yan awaren. A lokaci daya Putin ya jaddada suka a kan gwamnatin birnin Kiev inda ya ce ita ma tana da nata laifin game da faduwar jirgin saman, da ya hallaka mutane kimanin 300. A kuma halin da ake ciki an ba da rahoto gwabza kazamin fada a birnin Donetsk tsakanin dakarun gwamnatin Ukraine da 'yan tawaye da ke iko da birnin.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe