Mexiko za ta dakile bakin haure masu zuwa Amirka | Labarai | DW | 08.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mexiko za ta dakile bakin haure masu zuwa Amirka

Mexiko ta amince da bukatar Shugaba Donald Trump na AMirka kan dakile bakin haure masu shiga Amirka, lamarin da ya janyo soke kudaden fito da ake shirin saka wa Mexiko kan kayyakin da ake shigar da su Amirka.


Kasashen Amirka da Mexiko sun cimma yarjejeniya lamarin da ya kawar da saka kudaden fito ga kayayyakin da Mexiko ke kai wa zuwa Amirka. Karkashin yarjejeniyar Mexiko ta amince ta dakile bakin haure masu shiga Amirka, galibi daga kasashen Guatemala, Honduras da El Salvador  masu fama da tashe-tashen hankula, inda za su zauna a Mexiko har zuwa lokacin da aka tantance takardunsu na neman mafaka a Amirka.

Sakamakon wannan yarjejeniya an soke shirin Shugaba Donald Trump na Amirka na fara karban kudaden fito kan kayyakin Mexiko masu shiga Amirka daga ranar Litinin mai zuwa.