Merkel: ′′Za mu kara wa Chadi tallafi′′ | Labarai | DW | 12.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel: ''Za mu kara wa Chadi tallafi''

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana cewar kasarta za ta kara yawan tallfin da ta ke baiwa Chadi domin tinkarar kalubalen da ke gabanta musamman ma dai tada kayar baya ta 'yan ta'adda.

Merkel na wadannan kalamai ne lokacin da ta ke jawabi albarkacin ziyarar da shugaban Chadi Idriss Deby Itno ya kaimata a birnin Berlin, inda ta ce ''za mu samar da euro miliyan takwas da dubu dari 9 a matsayin tallafi ga Chadi don tinkarar matsalar ruwan sha da cimaka saboda kasar na kewaye da kasashen da ke fama da tashin hankalin da ya sanya ta karbar 'yan gudun hijira sama da dubu 700.''

Wani abu har wa yau da Merkel da Deby suka tabo yayin wannan ziyara tasa shi ne batun kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai wanda Shugaba Deby ya ce za a iya magance matsalar ce kawai idan kasashen Turai suka hada kai da dukannin kasashen da ke yankin Sahel maimakon tuntubar kasashe daban-daban.