1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel ta yi kira da a rufe sansanin Guantanamo

January 7, 2006
https://p.dw.com/p/BvDQ

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Amirka da ta rufe gidan yarinta na sansanin Guantanamo dake can kasar Cuba. A cikin wata hira da mujallar Der Spiegel shugabar gwamnatin ta ce bai kamata a bari wani sansani irin wannan ya ci-gaba da wanzuwa har na dogon lokaci ba. Amirka dai na tsare da daruruwan mutane da ta ke zargi da aikata ta´addanci a sansanin na Guantanamo, daukacin su kuwa ba´a gurfanad da su gaban shari´a ba. Merkel ta ce zata tabo wannan batu a tattaunawar da zata yi da shugaba GWB yayin ziyarar aikin da zata kai birnin Washington a mako mai zuwa.